ABNA24 : An dai kulla yarjejeniyar ce a lokacin tsohon shugaban kasar marigayi Janar Ibrahim Ba’are Mainasara.
Wasu kasashen masu makobtaka da Nijar din ne da suka hada da Chadi, Mali, Burkina Faso da Aljeriya suka shiga tsakani a locacin rikicin inda kuma aka sansanta jituwa tsakanin Abzinawa da ke dauke da makamai da kuma gwamnatin ta Nijar.
Tun dai lokacin ne a zagayowar ranar ta 24 ga watan Afrilu ake gudanar da bukukuwa domin kara hada kan al’ummar kasar.
A bana dai ana gudanar bikin ne a garin Agadas dake arewacin kasar, kuma wannan shi ne karon na 26.
342/